1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Akwai yiwuwar samun sakamakon farko

Zainab Mohammed Abubakar
July 4, 2020

Hukumar kula da lafiya ta MDD ta sanar da cewar, akwai yiwuwar samun sakamakon farko na gwajin maganin cutar COVID-19 nan da makonni biyu, a ta bakin babban Darektan WHO Tedros Ghebreyesus.

https://p.dw.com/p/3em6T
Symbolfoto Impfstoff
Hoto: picture-alliance/Geisler-Fotopress/C. Hardt

Sai dai shugaban bangaren agajin gaggawa na hukumar Mike Ryan ya ce, bai dace ayi hasashe lokacin da za a iya wadata al'umar duniya da allurar riga kafin cutar ta corona ba.

Akwai yiwuwar tabbatar da sahihancin allurar a karshen wannan shekarar, amma ayar tambayar a nan ita ce, yaushe za a iya sarrafa adadadin da zai wadata jama'a? a cewar Ryan a taron manema labaru.

A fadin duniya dai, yanzu haka kusan mutane miliyan 11 suka kamu da kwayar cutar ta COVID 19, a yayin da sama da dubu 523 daga cikinsu, suka rasa rayukansu.