1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Azumi cikin annobar Coronavirus

Lateefa Mustapha Ja'afar
April 23, 2020

Yayin da ake shirin fara azumin watan Ramadana na bana, annobar Coronavirus da duniya ke ciki ta tilasta dakatar da wasu ayuukan da aka saba gudanarwa cikin azumin irin su jam'in sallar tarawi a Masallatai da tafsiri.

https://p.dw.com/p/3bKhe
Nigeria Ramadan
Babu jam'in tarawi da tafsiri a azumin banaHoto: picture alliance/AA/M. Elshamy

A wannan shekarar, al'ummar Musulmi a fadin duniya sun riski watan azumin Ramadana, cikin fargaba da tashin hankali na annobar Coronavirus da duniya ta tsinci kanta a ciki. Annobar dai ta janyo rufe Masallatai da makarantu, inda har ma aka rufe manyan Masallatai biyu da ke kasar Saudiyya. Rahotanni dai sun nunar da cewa mahukuntan Saudiyyan sun dakatar da zuwa ziyarar Ummara, da a bisa al'ada Musulmi daga fadin duniya ke kai wa musamman a lokacin watan Tamadan.

Haka ma abin ya ke a sauran kasashe, misali a nahiyar Afirka, inda a Najeriya aka hana zuwa Masallatai na Jumma'a da ma halartar Masallatan domin gudanar da sallar Tarawi a lokacin Azumi da kuma tarurrukan tafsiri, da a bisa al'ada aka saba gudanarwa duk shekara, a lokacin azumin na watan Ramadana.