1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar kulle don yaki da coronavirus

Abdoulaye Mamane Amadou
October 14, 2020

Hukumomi a Faransa sun bayyana daukar muhimman na kakaba dokar kulle daga karfe 9:00 zuwa 6:00 na safe a sassan kasar da ke fama da kamarin annobar corona ciki har da birnin Paris kama daga ranar Asabar.

https://p.dw.com/p/3jwWg
Deutschland will 662 Millionen Dollar an Hilfe für Holocaust-Überlebende geben
Hoto: Gil C. Magen/Photoshot/picture alliance

Shugaba Emmaneul Macron da kansa ne ya ambaci haka a dazu-dazun nan a yayin da yake ganawa da 'yan jarida a wata tattaunawa ta musamman kan muhimman matakan gwamnatin kasar ame da kamarin da cutar ke yi a wasu yankuna.

Shugaba Macron ya ce wa'adin dokar kullen zai kasance ne na makwanni hudu a matakin farko, kan daga bisani majalisar dokokin kasar ta bayar da sahalewarta na sake tswaita wa'adin har zuwa farkon watan Disamba adadin makwannin shidan kenan da shugaban yace yana mai yakinin cewa zai iya taimaka wajen takaita sake yaduwar cutar.