1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maganin gargajiya don yaki da corona

Abdullahi Maidawa Kurgwi
June 5, 2020

Masu maganin gargajiya a Najeriya na ikirarin suna da maganin cutar Corona. Shirin lafiya jari ya duba kudirin gwamnatin Najeriya na fara gwajin magungunan gargajiya ko za’a yi dacen maganin cutar ta corona

https://p.dw.com/p/3dJfz
Karikatur: Nigeria Covid-19, Lassa, Ebola
Hoto: DW/A. B. Aminu

Wasu kasashen Afrika sun fara tunanin fadada bincike don samun maganin cutar corona ta hanyar  magungunan  gargajiya, inda  kasar madagaska ta soma raba wa kasashen Afrika magungunan da ta gano don maganin cutar Covid 19.

Gwamnatin Najeriya ita ma ba’a  barta a baya ba, ta umurci ma’aikatar lafiya ta kasar da ta karbi magugngunan gargajiya a hanun  masu magungunan na gida don soma gwaji kan wannan cuta. 

Ko ya ya likitocin gargajiyan na Najeriya suka karbi wannan kira na gwamnati?

A saurari wannan shiri na lafiya Jari.