1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina: Wariya yayin yakar coronavirus

May 12, 2020

'Yan kasashen Afirka kimanin dubu 15 ke zaune a birnin Guangzhou, cibiyar hada-hadar kasuwanci a kasar Chaina. A farkon watan Afrilu an kore su daga gidajen haya, an kuma killace su a dole da sunan yaki da cutar corona.

https://p.dw.com/p/3c7XY
Textilindustrie in China neu
Ana hana bakaken fata shiga wurin aiki a masana'antun GuangzhouHoto: picture-alliance/dpa

Ko da yake yanzu abubuwa sun lafa a birnin na Guangzhou kuma mahukuntan Chaina sun amsa cewa sun tabka kurakurai, amma matakan da ake dauka dangane da corona sun nuna a fili yadda ake fama da matsalar wariyar launin fata a Chaina. A wata ma'aikatar sarrafa tufafi da ke Guangzhou din, an hana baki ma'aikata shiga ciki. Ga tunani da yawa na al'ummar Guangzhou, baki musamman bakaken fata na da babbar kasadar yada kwayar cutar coronavirus fiye da 'yan Chaina.

Cin zarafin bakaken fata

A farkon watan Afrilu ya fito fili yadda 'yan Najeriya da dama suka kamu da cutar a birnin na Guangzhou, saboda haka mazauna da ma mahukunta a birnin sannu a hankali suka rika daukar matakan ba sani ba sabo kan baki. Buba wani matashi ne dan shekara 21 daga kasar Gambiya da ke yammacin Afirka, da ya ce wani abokinsa ya buga masa waya yana gargadinsa yadda ake kame 'yan Afirka a birnin.
An dauki kwanaki ana cin zarafin bakaken fata a Guangzhou, ana korar su daga gidan haya, a gidajen abinci, an rataya alluna da ke cewa an haramtawa bakar fata shiga. Akalla sau hudu a shekara Buba kan je Guangzhou domin harkar kasuwancin tufafi da takalma. Tun a karshen watan Janairu ya makale a birnin, saboda matakan hana tafiye-tafiye domin yakar cutar.

Bildergalerie Ausstellung Baohan Street: An African Community in Guangzhou
Gidajen abinci sun daina barin bakaken fata su shigaHoto: Li Dong

A cikin watan Afrilun ne kuma aka killace shi a dole, duk da cewa ba shi da alaka da 'yan Najeriyar da suka kamu da cutar. Ga abin da Buba ke cewa: "Sun kori abokina daga otel din da yake, ni ganau ne ba jiyau ba. 'Yan sanda sun fada masa dole dukkan bakaken fata su bar otel din nan-take. Na yi fushi sosai. Ba daidai ba ne a killace mutane ba tare da an fada musu abin da ke damunsu ba. Mu duka mutane ne, launin fatarmu kadai ya bambanta da na su. 'Yan Chaina na zargin bakar fata da yada kwayar cutar. A ganinsu duk 'yan Afirka muna da dangantaka da juna, amma ba haka abin yake ba.

Geoffrey Onyeama und Zhou Pingjian
Ministan kasashen waje na Najeriya Geoffrey Onyeama da jakadan Chaina a kasar Zhou Pingjian Hoto: DW/Uwais Abubakar Idris

Tsugune ba ta kare ba

Yanzu haka dai mahukunta a Guangzhou sun amsa cewa sun tabka kurakurai a matakan da suka dauka kan bakin, saboda haka sun gabatar da sababbin dokoki. A dole shugabannin kasa da na jam'iyyar da ke jan ragamar mulki sun mayar da martani, inda suka yi fatali da zargin wariyar fata, a lokaci guda kuma suka yi tir da nuna wariya ta kowane fanni. Sai dai abin da ke faruwa a zahiri ya sha bamban kamar yadda aka ji wani direban tasi na fada. "Ba ma tunanin daukar fasinja bakar fata. Muna daukar farar fata matukar suna tare da 'yan Chaina. Amma duk wani farar fata da ya zo shi kadai, ba ma daukarsa a tasi. Bakar fata ma gaba daya ni ba na daukarsu, saboda rashin tsabtarsu."

Nuna wa bakar fata wariya ba sabon abu ba ne a Chaina, sai dai cutar corona ta kara fito da matsalar fili. Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch, ta dade tana sukar wariyar launin fata a Chaina da kuma yin kira ga mahukuntan kasar da su dauki matakan kawo karshenta.