COVID-19: An sassauta dokar kulle a duniya | Zamantakewa | DW | 07.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

COVID-19: An sassauta dokar kulle a duniya

Kasashen duniya da dama sun sassauta dokar zaman gida da suka sanya domin dakile yaduwar annobar coronavirus da ta addabi duniya baki daya.

Spanien Menschen gehen zurück zur Arbeit

Bayar da tazara da saka takunkumin fuska, bayan sassauta dokar kulle.

Al'amura sun tsaya cak haka ma harkokin kasuwanci sun raunana a duniya, sakamakon dokar zaman gida da kasashen duniya da dama suka assasa domin rage yaduwar annobar cutar coronavirus ko kuma COVID-19 da ta yi wa duniya tsinke.

Koda yake a kasashen Afirka misali Najeriya, masana kiwon lafiya na ganin tamkar an yi garaje wajen saukaka dokar zaman gidan. Matsalar da aka fi fuskanta a nahiyar Afirkan dai shi ne, rashin kiyaya ka'idoji ko kuma matakan kare kai.

Bayar da tazara da kuma sanya takunkumin hanci, na daga cikin ka'idojin da aka gindaya, misali a Jamus da sauran kasashen da suka ci gaba. Sai dai a kasashen Afirka, zai yi wahala abi ka'idojin musamman ma na bayar da tazara da gujewa cunkoso.

DW.COM