Coronavirus: Najeriya ta amince a bude wuraren ibada | Labarai | DW | 01.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Coronavirus: Najeriya ta amince a bude wuraren ibada

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta sassauta dokokin da ta dauka na yakar Coronavirus inda yanzu ta bayar da umarnin a sake bude wuraren ibada sannan a bai wa jiragen sama izinin zurga-zurga a cikin kasar.

Bayan share tsawon lokaci cikin halin kunci a Najeriya a sakamakon daukar matakan hana yaduwar cutar Coronavirus, yanzu gwamnati ta sassauta dokokin da ta dauka inda ta bayar da umarnin a sake bude wurare na ibada sannan a bai wa jiragen sama izinin zurga-zurga a cikin kasar.

A karo na biyu na kokarin tunkarar annobar Covid-19 din dai gwamnatin Najeriya ta aiyana bude Masallatai da Coci-coci domin gudanar da ibada sannan kuma da  sanar da fara jigilar fasinjoji  ta jiragen sama daga 21 ga wannan watan na Mayu  da muke ciki. Cikin kashi na Biyu na kokarin saukaka lamuran dai har ila yau gwamnatin Najeriyar ta dage killacewar da ta yi wa jihar Kano da ke zaman daya a cikin muhimman cibiyoyin annobar cutar a kasar. 

To sai dai kuma a  cikin wani jawabin da shugaban kwamitin yakar annobar tarrayar Najeriyar, Boss Mustapha ya karanta, makarantu za su cigaba da kasancewa a rufe har na tsawon wasu makonni hudu masu zuwa, duk da cewar gwamnatin kasar ta amince a bude harkoki na kasuwa a ko'ina cikin kasar in har sun cika ka'ida ta yakin cutar.Sannan an haramta taron da ya wuce mutane ashirin in banda wuraren aiki, dage haramcin da aka yiwa wurare na ibada tare da cika ka'idar da kwamitin ya shimfida.

Haramcin zurga-zurga daga wata jiha zuwa wata  in banda kayayaki na abinci da hajjar man fetur da kayayyakin da aka sarrafa da kuma kayyayaki na bukatu sannan kuma da tilasta amfani da takunkumin rufe fuska a cikin bainar jama'a, sannan, kuma da tilasta amfani da man wanke hannu a ko'ina a bainar jama'a. Matakin da ke zaman na biyu da kuma zai share tsawon makonni guda hudu dai zai kuma kalli bude wasu tashoshi na jirage na sama guda hudu da suka hada da Kano da Abuja da Legas da kuma fatakwal. Ana kuma sa ran jiragen za su fara tashi ne kawai daga tashoshin daga ranar 21 ga watan junin da muke ciki.

An kuma bai wa bankuna damar aiki na kwanaki biyar a yayin kuma da a kara tsawon aiki na gwamnati daga kwananki uku ya zuwa Biyar domin bai wa maikata da ke mataki na 14 zuwa sama damar aiki kullum. An haramta gidajen barasa da gidajen motsa jiki. Ana sa ran jihohi na kasar za su taka muhimmiyar rawa a cikin sabo na matakin da ke zaman kama hanyar komawar lamura daidai a kasar. Tun a watan Maris din da ya shude ne dai tarrayar Najeriyar ta kai ga kulle kanta da nufin tunkarar annobar da yawanta ya haura dubu 10,000 a yanzu.