1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar coronavirus na lakume rayuka

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 13, 2020

Bayan sama da watanni biyu da bullar kwayar cutar coronavirus, da ta bulla a kasar Chaina da kuma ke yaduwa cikin gagawa, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sauya mata suna zuwa Covid 19.

https://p.dw.com/p/3Xk6X
China Wuhan Jinyintan Hospital
Matakan kare kai daga kamuwa da cutar coronavirus ko covid 19 Hoto: picture-alliance/AP/Chinatopix

Ita dai kwayar cutar ta coronavirus ko kuma covid 19 kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sauya mata suna cikin wannan makon, ta fara bulla ne a garin Wuhan na kasar Chaina, kuma a halin yanzu ta halaka mutane sama da 1,000 a Chainan. Tuni dai kasashen duniya ciki har da na Afirka ke bayyana cewa suna daukar matakan da suka dace domin dakile yaduwarta zuwa kasashensu. KWayar cutar dai na saurin yaduwa tare kuma da yin kisa.