1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cutar Coronavirus na yin barna a Amirka

Usman Shehu Usman
April 3, 2020

Kasar Amirka na cikin wani masifar da ba a shiga irinta ba a shekarun baya-bayannan inda yanzu haka Amirkan ke da mutane sama da 261 wadanda annobar Corona ta kama.

https://p.dw.com/p/3aQVQ
Coronavirus USA Los Angeles medizinisches Personal Proteste gegen schlechte Ausstattung
Hoto: AFP/R. Chiu

Kawo yanzu dai sama da mutane 6.700 suka mutu a fadin kasar ta Amirka, yayinda a birnin New York kadai mutane sama dubu 57,000 suka kamu da cutar, inda sama da 1.5 suka mutu a bhirnin, wanda ya fi shiga tashin hankalin Coronavirus. Gwamnan jihar da magajin garin birnin na New Yorka sun bada umarnin asibitoci su sallami mutanen da ke jinya wace ba ta Coronavirus ba domin a barwa asibitotcin masu fama da Coronavirus kadai. Wata babbar matsalar Corona da fada wa Amirka ita ce, yadda hatta jirgin ruwansu mai dakon jiragen sama, wandanda yanzu ke a yankin Asiya, cutuar Coronavisu ta harbi sojoiin, inda kawo yanzu sojoji  kimanin 120 aka tabbatar sun harbu ta cutar, yayinda tun farko kwamandan jirgin ruwan ya yi gargadin cewa dakarunsa za su fada cikin masifar Corona, abin da ya sa aka sallame shi da cewar ya yi azarbabi. 

A kasashen yammacin Afirka ma annobar Corona na ci gaba da yaduwa, inda a Kasar kamaru mutanen 306 suka kamu, Ghana 205, Najeriya 190, Nijar 98 sai kuma Chadi mutane 8 suka harbu da cutar ta Corona kawo lokacin da muke rubuta wannan labarin.