1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona za ta raba yara miliyan 10 da karatu

Gazali Abdou Tasawa
July 13, 2020

Wani rahoton kungiyar agaji ta Save the Children ya bayyana cewa yara sama da miliyan 10 na fuskantar barazanar kasa komawa makaranta a duniya bayan dage dokar kulle ta Covid-19.

https://p.dw.com/p/3fDZM
Save the Children - Uganda Schule in in Nakasongola
Hoto: Andrew Pacutho/Save the Children

Kungiyar agaji ta Save the Children ta ce yara sama da miliyan 10 ne ke fuskantar barazanar kasa komawa makaranta kwata-kwata a duniya bayan dage kulle a bisa dalillai na matsalar tattalin arziki da annobar cutar Coronavirus ta haifar.

A wani rahoto da ta fitar a wannan Litinin kungiyar ta kasar Birtaniya ta ce dama tun kafin bayyanar annobar cutar ta Covid 19, akwai yara da matasa miliyan 258 da ba sa zuwa makaranta a duniya. 

Kuma da cutar ta Corona ta bayyana sai da ta tilasta wa yara da matasa kimanin miliyan dubu daya da dari shidda dakatar da zuwa makaranta. Rahoton ya ce wannan shi ne karon farko a tarihin duniya da wata matsala ta dagula harkar ilimin yara a duniya baki daya.

Rahoton ya ce idan har gwamnatoci da masu hannu da shuni ba su kawo wa fannin ilimi agaji ba a cikin gaggawa, to kuwa nan zuwa karshen shekara yara kusan miliyan 10 akasarinsu 'yan mata za su kasa komawa makaranta har abada.