1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dakatar da wasannin Bundesliga saboda Corona

March 13, 2020

Hukumar wasannin kwallon kafa ta Jamus  DFL ta dakatar da wasannin Bundesliga har zuwa ranar biyu ga watan Afrilu.

https://p.dw.com/p/3ZNbU
Fussball, Bundesliga | Borussia Mönchengladbach - 1. FC Köln
Hoto: picture-alliance/dpa/U. Hufnagel

A karon farko a tarihin wasannin Bundesliga na Jamus a wannan makon an gudanar da wasanni ba tare da 'yan kallo a filayen kwallo ba. A waje guda kuma mahukunta sun ce an jingine wasannin a sakamakon tsoron yaduwar cutar Coronavirus. Dakatar da wasannin ya shafi har da wasannin da aka shirya gudanarwa  a karshen makon nan.

Wasa ba tare da 'yan kallo ba

Kafin mahukunta su sanar da dakatar da wasannin kwallon kafar na Bundesliga sai da aka fara daukar matakin yin wasu wasanni ba tare da 'yan kallo ba. 

Yaduwar cutar coronavirus a Jamus ta kama hanyar zame wa Borussia Dortmund ala-kakai bisa la'akari da kawar da ita da kungiyar PSG ta yi a gasar zakarun Turai a ranar Laraba. Sannan kuma karawar da za ta yi da 'yar uwarta Schalke 04  a mako mai zuwa yanzu an soke ta. An yi wa wasan nasu lakabi da "uwar wasannin Bundesliga" sai dai kuma yanzu mahukunta sun ce wasan ba zai gudana ba. Magoya bayan kungiyoyin biyu su na ganin wannan taron shi ne mafi muhimmanci a wannan lokacin. Hakan na nufin cewa filin wasa na Signal Iduna Park mai daukar mutane 82,000 zai kasance babu 'yan kallo saboda fargabar yaduwar cutar coronavirus, lamarin da zai zama koma baya ga kungiyoyi hatta ma a fannin tattalin arziki.

Fußball Bundesliga Schalke 04 v Borussia Dortmund
Dan wasan Schalke 04 da Borussia Dortmund a filin wasa a shekara ta 2019Hoto: Imago Images/Kolvenbach

A baya Ministan Lafiyar na Jamus, Jens Spahn, ya bukaci da a soke duk wani taro ko gangami da zai hada sama da mutum 1000 a fadin kasar, har sai abin da hali ya yi. Wasu kungiyoyin wasanni sun nuna turjiya da farko amma daga bisani suka mika wuya ta la’akari da barazanar cutar. Sai dai kungiyoyin ba su kai ga fara mayar da martani a kan matakin soke wasannin gaba-daya da mahukunta suka yi a wannan Juma'ar ba.

Kungiyar Mönchengladbach ta kafa tarihi inda ta doke Köln FC da ci 2-1 a wasa na farko na Bundesliga ba tare da 'yan kallo ba. Sai dai  a karshen makon nan wasan da aka tsara gudanarwa a tsakanin kungiyar Marcus Thuram tare da Eintracht Frankfurt  a ranar Lahadi ba zai gudana ba saboda dakatar da wasannin Bundesliga da mahukunta suka yi.

Tun kafin a kai ga daukar wannan mataki, mai kula da kungiyar Borussia Mönchengladbach, Max Eberl, ya ji takaicin yin wasanni ba tare da 'yan kallo a filin wasa ba.

"Mun fahimci cewar ya kamata a dauki matakan dakatar da yaduwar wannan cuta. Lallai za mu ji shi ba dadi, sai dai babu yadda muka iya. Ya zame mana tilas mu yi wasan a haka ba tare da ‘yan kallon ba." inji Max Eberl

Oscar Wendt shi ne ke tsare wa kungiyar  Mönchengladbach baya. Ya ce wasannin Bundesliga sun shiga wani hali a sakamakon cutar Coronavirus.

"Abin babu armashi, wasa ba tare da dandazon ‘yan kallo ba. Don kuwa suna daga cikin dalilan da suka sanya mini musamman sha’awar kwallo tun da fari, har kuma na fara taka leda. Burinmu ne tun muna kanana wasa a manyan filayen wasannin" inji Oscar Wendt

Fußball Bundesliga Union Berlin vs VFL Wolfsburg Spielunterbrechung Plakat gegen Dietmar Hopp
Yan kallo ke nan a lokacin da ake wasa a tsakanin Union Berlin Wolfsburg a farkon watan Janairu 2020Hoto: picture-alliance/dpa/A. Gora

Kungiyar da ta fi takaicin rashin 'yan wasa a filin kwallo ita ce Union Berlin wadda ta saba dogara da tsayar da tsumi daga magoya bayanta 22,000 wajen tabuka abin kirki a Bundesliga. To sai dai wasanta da aka shirya a wannan Asabar a tsakaninta da yaya-babba Bayern Munich ba zai gudana ba saboda dakatar da wasannin Bundesliga da mahukunta a Jamus suka yi. Idan za a iya tunawa dai Union Berlin ta doke Dortmund da Mönchengldbach a baya. Masu sharhi dai na ganin rufe filayen kwallon Bundesliga zai bakantawa 'yan wasa da masu kallo da magoya bayan wadannan kungiyoyi da ke sassa dabam-dabam na duniya.