1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma Paparoma ya bukaci tsagaita wuta a duniya

Usman Shehu Usman
March 29, 2020

 Yayin da annobar Coronavirus ke kara yaduwa a duniya shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya bukaci a dakatar da daukacin yake-yake da ke farawa a fadin duniya.

https://p.dw.com/p/3aAkA
Vatikan Coronavirus |  Papst Franziskus spricht sein wöchentliches Angelus-Gebet
Hoto: Reuters/C. Casilli

  Da yake jawabin ranar Lahadi da ya saba yi, Paparoma ya ce duba da yadda annobar Corona ke yaduwa a duniya, akwai matukar bukatar dakatar da duk wani rikici a duniya don bai wa iyalai zama gida. Paparoma ya tabo musamman barikokin soja da sansanonin 'yan gudun hijira da muta ne dake gidajen yari, a matsayin wadanda ake matukar bukatar su samu damar zuwa gidajensu don gudun kamuwa da cutar Corona, wace cuncoson jama'a ke kara yada ta. Shugaban darikar Katholikan dai ya nuna goyon bayansa ne ga sakatare janar na MDD Antonio Guterres, wanda ya bukaci a tsagaita wuta a yakin da ke faruwa a kasar Siriya. Inda yakin ke haddasa karuwar 'yan gudun hijira baya ga dubbai da ake da su yanzu.