Corona: Najeriya ta rufe dukkan filayen jiragen sama | Labarai | DW | 21.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

An hana saukar jiragen waje a Najeriya

Corona: Najeriya ta rufe dukkan filayen jiragen sama

Gwamnatin Najeriya ta sanar a yammacin wannan Asabar cewa ta rufe manyan filayen jiragen samanta na Abuja babban birnin kasar da na Legas wanda ke zama cibiyar kasuwancin kasar.

Hukumomi sun dauki matakin ne biyo bayan samun karuwar masu dauke da cutar Coronavirus wadda kawo yammacin ranar Asabar mutane 22 ke dauke da ita a kasar. 

Matakin rufe filayen jiragen saman na Legas da Abujan wadanda sune kadai da gwamnatin ba ta rufe wa jiragen kasashen duniya ba, zai fara aiki daga ranar Litinin 23 ga watan nan na Maris. 

Nigeria Nnamdi Azikiwe International Airport in Abuja

Jama'a a filin jirgin saman Abuja na Najeriya a wani hoto da aka dauka a 2013

 

Henrietta Yakubu ita ce mai magana da yawun hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya. Ta kuma shaida wa wakilinmu na Abuja Uwais Abubakar Idris cewa karuwar cutar Coronavirus ce ta sa aka dauki wannan mataki.

Hukumomi dai sun ce za a dauki tsawon wata guda ana hana jiragen sama daga kasashen waje zuwa Najeriyar. Sai dai za a iya bude kofa idan aka samu bukata ta gaggawa.