Cop23: Fiji za ta kauradda kauyuka 40 | Labarai | DW | 17.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cop23: Fiji za ta kauradda kauyuka 40

Tumbatsar Teku ya tilasata wa mutane da ke cikin kauyukan da ke gabar ruwa kaurar gaggawa zuwa yankuna da ke kan tudu, matakin ake ganin zai tsiradda rayuka da dukiyoyi daga amabliya.

Kasar Fiji na shirin shirin samar da matakan taimakawa sauran mutanen da ke yankin Pacific da za su iya fuskantar barazanar tumbatsar Teku anan gaba, hukumomin tsbirin Fiji na jagorantar kasashen duniya akalla 200 a babban taron MDD kan sauyin yanayi a kasar Jamus.

Kasar na shirin samar da nagartaccen hanyar kare sauyin yanayi da ke haddasa narkewar duwatsun kankara, kazalika kasar na aiki tukuru na ganin an warware matsalolin da suka shafi hakkin mallakar filaye da samun 'yanci zama dan kasa.