Conde: Babu shirin dage zabe a Guinea | Labarai | DW | 09.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Conde: Babu shirin dage zabe a Guinea

Shugaban kasar Guinea ya ce babu gudu babu ja da baya a shirin zaben kasar duk da korafin da 'yan adawa ke yi cewar shirin zaben na cike da kura-kurai.

Guinea Präsident Alpha Conde

Shugaba Alpha Conde

Shugaban kasar Gini Alpha Conde ya bayyana cewa babu wani shiri na dage zaben da kasar ta tsara yi a karshen mako, inda ya yi watsi da bukatar 'yan adawa ta ganin an dage zaben bayan da magoya bayan bangarorin biyu suka gwabza fada a birnin Conakry. Fadan da aka yi yammacin ranar Alhamis ya yi sanadin halaka mutum guda wasu sama da 20 suka sami raunika.

Masu adawa da shirin zaben dai tsawon watanni na cewa akwai kura-kurai da dama a shirin zaben, don haka suka bukaci a dage zaben shugaban kasar da za a yi a karshen mako. Ita kuwa hukumar da kan tsara zaben CENI ta ce ta shirya tsaf don gudanar da zabe a kasar ta Guinea Conakry . Masana dai da kan yi sharhi a kan zaben kasar na nuni da cewa da wahala a rasa rikici da zai biyo bayan zaben.