Compaoré ya tsira daga tuhumar cin amana | Labarai | DW | 30.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Compaoré ya tsira daga tuhumar cin amana

Babban mai shigar da kara na Burkina Faso ya ce tsarin mulki bai tanadi hukunci a kan laifin cin amanar kasa da tauyen kundin tsarin mulki ba, saboda haka ba za a tuhumi tsohon shugaba Blaise Compaoré da wannan laifi ba.

Babbar kotun Burkinsa Faso ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa tsohon shugaban kasa Blaise Compaore na cin amanarsa kasa da tauyen kundin tsarin mulkin, saboda babu wani tanadi da tsarin shari'ar kasarsa ya yi dangane da wadannan laifuffuka. Babban mai shigar da kara na wannan kotu Armand Ouedraogo ne ya yi wannan bayani a wani taron manaima labarai da ya gudanar a Ouagadougou babban birnin Burkina Faso.

Sai dai ya jadadda cewar Blaise Compaore wanda ya shafe shekaru 27 a kan kujerar mulki zai fuskanci shari'a a matsayin tsohon ministan tsaro sakamakon cin zarafin al'umma lokacin tayar da kayar baya da ta biyo bayan yunkurinsa na yin tazarce. Sannan kuma zai gurfana gaban kuliya dangane da zargin da ake yi masa na marar hannun a kisan da aka yi wa tsohon shugaban kasa Thomas Sankara lokacin da aka yi masa juyin mulki.

A yanzu haka dai Blaise Compaore na gudun hijira a kasar Côte d 'Ivoire. Ya yi niyar gudanar da salon mulkin sai madi ka ture bayan wa'adi hudu na mulki, lamarin da ya tunzara al'ummar Burkina Faso ga yin more tare da kawo karshen mulkinsa