Cocin Jamus za ta ceto bakin haure | Labarai | DW | 13.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cocin Jamus za ta ceto bakin haure

Cocin Protestant a Jamus, ta ce za ta aike da jirgin ruwa don ceto bakin haure a tekun Bahar Rum, wadanda suka makale a kokarinsu na shiga nahiyar Turai.

Shugaban cocin na Jamus, Heinrich Bedford-Strohm, shi ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis a wani sako na majalisar gudanarwar darikar ta Protestant.

Sanarwar ta kuma zo ne bayan gabatar da bukatar ganin an yi hakan da manyan ikilisiya suka yi a farkon wannan shekara.

Cocin ta kuma ce tana shirin zama da shugabannin kasashen Turai don daukar mataki kan matasalar bakin na haure.

Tsawon shekaru ne dai cocin na Protestant ke kokarin kawo karshen matsalolin da ke sanya bakin haure daga nahiyar Afirka ke barin kasashen na su, a cewar malamin na addini, Bedford-Strohm.