1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cinikin makamashin Rasha zuwa Ukraine

January 14, 2015

Kungiyar EU ta bayyana cewa za ta ci gaba da shiga tsakani kan cinikin makamashin Rasha da Ukraine musamman a lokacin da ake kwarara sanyi a Turai.

https://p.dw.com/p/1EKeV
Ukraine Gas Import aus der Slowakei 02.09.2014
Hoto: Reuters

Ministan harkokin makamashi na kasar Rasha Alexander Novak ya bayyana cewa babu wani dalili da zai sanya a samar da sauyi a sharudan samar da makamashi a kasar Ukaraine idan sharudan da ake kai yanzu suka kammala cika aikinsu a karshen watan Maris na shekarar 2015.

Maros Sefcovic kwamishinan makamashi a Kungiyar EU yayin ganawarsa da Mista Novak a birnin Moscow ya bayyana cewa kungiyar za ta ci gaba da zama mai shiga tsakani da kan tattaunawar da ake tsakanin kasar ta Rasha da Ukraine.

Sefcovic ya ce ba za a kuma samar da tangarda ba kan shirin samar da iskar gas daga Rasha zuwa kasashen Turai da kan ratsa kasar Ukraine cikin aikin dasa sabon bututu tsakanin kasashen da zai kewaye kasar ta Ukraine.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal