Cin zarafin masu zanga-zanga a Yemen | Labarai | DW | 28.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cin zarafin masu zanga-zanga a Yemen

Bayan harba alburusai a samaniya da ma dukan masu zanga-zangar da kulake da sukan wasunsu da wuka, mayakan na kama mutane suna tsarewa.

'Yan tawaye da ke da iko da birnin Sana'a fadar gwamanatin kasar Yemen sun fatattaki wasu masu zanga-zanga lokacin da suke gangamin nuna musu adawa inda suka tarwatsasu ta hanyar harba alburusai a samaniya da ma dukan masu zanga-zangar da kulake da ma saran wasunsu da wuka.

Wani da ya ga yadda lamarin ya faru ya ce 'yan tawayen da ake kira Houthi sun kame masu zanga-zanagr da dama ciki kuwa har da 'yan jarida sannan wasu mutanen sun sami raunika a yayin zanga-zangar.

Wata jaridar kasar ta Yemen da ke bada labaranta ta kafar intanet ta bayyana cewa ita ma mayakan na Houthi sun kame musu jami'insu, kuma ta bayyana cewa duk abinda ya sami wannan dan jarida to kungiyar ce zata dauki alhaki.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Pinado Abdu Waba