1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin zarafin bakin haure a wakafi a Libiya

June 24, 2014

Binciken da Kungiyar Human Right Watch ta gudanar ya nunar da cewar ana musguna wa bakin haure da 'yan ci-rani da masu neman mafakar siyasa a gidajen yarin Libiya.

https://p.dw.com/p/1CPKe
Hoto: Sara Prestiani

Fursunoni 138 jami'an Human Right Watch suka tattauna da su kan halin da suka ciki a gidajen yari kasar Libya. Sai dai 100 daga cikinsu sun bayyana musu cewa suna fuskantar cin zarafi iri daban daban daga gadurobobin wannan kasa. Su bakin hauren suka ce ana lakaba musu dan karen duka ba tare da wani tartibin dalili ba. Sannan kuma gandurobobi na konasu da karar taba sigarin da suke kunnawa. Kai, cin zarafin ma ya kai nuna wariyar jinsi da na launin fata, da kuma uwa uba yi wa matasa da mata tsaraici ko kuma caje daukacin jikinsu. Sai dai kuma abin mamakin a cewar Gerry Simpson da ke zama daya daga cikin wadanda ya gudanar da binciken, shi ne hadin kai da suka samu daga hukuomin Libiya

Babban abin takaicin ma dai a cewar Human Right Watch, shi ne rashin tsawatawa daga hukumomin Libiya, alhali dokokin kasa da kasa sun tilasta musu kare fursunoni daga cin zarafi. Hakazalika ba a bai wa bakin hauren da masu neman mafakar siyasa a Libiya kulawa da ta dace a fannin kiwon lafiya, alhali gidajen yarin kasar na samun tallafi daga hukumomin EU da kuma na Italiya. Saboda haka ne Gerry Simpson na HRW ya ke neman Libya da ta bai wa Majalisar Dinkin Duniya damar kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin gaskiya ta yi halinta.

Libyen Flüchtlinge von italienischer Marine gerettet
Matakai ba sa hana bakin hauren Libiya tsallkawa ItaliyaHoto: REUTERS

Dubban 'yan Afirka ne ke zuwa Libiya don samun aikin yi ko kuma neman tsallakawa nahiyar Turai ta barauniyar hanya da nufin neman inganta halin rayuwarsu. Ma'aikatar kodago ta wannan kasa ta nunar da cewa a shekara ta 2004 kawai kimanin bakin haure miliyan uku ne Libiya ta kunsa. Sai dai kuma duk matakan da ake dauka na ja musu burki, ba ya hana hakar wasu daga cikinsu cimma ruwa. Ko da a watanni hudu na baya-bayannan sai da wasu 'yan Afirka dubu 42 suka bi Libiya wajen shiga Italiya ta barauniyar hanya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Pinado Abdu-Waba