Cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Ukraine | Labarai | DW | 23.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Ukraine

'Yan awaren gabashin Ukraine sun amince da tsagaita bude wuta na tsahon kwanaki biyar a kokarin shawo kan rikicin da aka shafe watannin ana fama da shi a kasar.

Shugabannin manyan bangarorin awaren gabashin Ukraine biyu ne suka bayyana amincewarsu da tsagaita wutar zuwa ranar Jumma'a nan 27 ga watan Yunin da muke ciki.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar Alexander Boroday ne ya bayyana hakan bayan wata tattaunawa da suka yi da jakadan Rasha a Ukraine da tsohon shugaban kasar da kuma wakilin kungiyar tsaro ta nahiyar Turai OSCE. Boroday ya ce jagororin yankunan Luhansk da Donetsk sun amince da su tsagaita wuta a nasu bangaren.

Da ma dai tun a makon da ya gabata sabon shugaban kasar ta Ukraine ya yi kiran tsagaita wuta na mako guda inda ya umurci bangaren dakarun gwamnati da su dakatar da bude wuta a kan 'yan awaren.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe