1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar yarjejeniya tsakanin kasashen Kenya da Yuganda

Kamaluddeen Sani/ LMJAugust 10, 2015

Ƙasashen Kenya da Yuganda sun kai ga cimma wata yarjejeniyar sanya bututun mai da zai haɗe da sababbin rijiyoyin man fetur ɗin da aka gano a ƙasar Kenya.

https://p.dw.com/p/1GD16
Yunkurin shimfida bututun man fetur.
Yunkurin shimfida bututun man fetur.Hoto: picture-alliance/ dpa

Wannan yunƙurin dai wani mataki ne da zai kai ga cimma yarjejeniyar ƙarshe a kan rijiyoyin man fetur ɗin kamar dai yadda shugabanin ƙasahen biyu suka bayyana.

Tun da fari dai sai da shugabanin ɓangaren man fetur ƙasashen biyu suka bayyana fargabar cewar ba za su iya kai wa ga cimma yarjejeniyar ba sakamakon wani sabon bincike da ake yi a ƙasashen Yuganda da Kenyan har sai an bayyana adaadin kuɗaɗen da aikin shimfiɗa bututun zai laƙume.

Yuganda dai ta kiyasta cewa aƙalla ta na da gangar danyan mai miliyan 6,500 a rijiyoyin manta yayin da Kenya ke da kimanin ganga miliyan 1000.