1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta cika shekara da samun sauyin mulki

Usman Shehu Usman
April 10, 2020

An cika shekara da kifar da gwamnatin kama-karya ta tsohon shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir, inda sannu a hankali kasar ta kama hanyar dorewa kan tafarkin dimukuradiyya.

https://p.dw.com/p/3akp3
Sudan Khartum | Prozess & Urteil Omar al-Baschir, ehemaliger Präsident | Anhänger
Hoto: Getty Images/AFP/A. Shazly

Kasar Sudan wacce ke farfadowa bayan kifar da gwamnatin kama-karya na fuskantar kalubale wajen yaki da Coronvirus, wandda ta jawo nakasu ga tattalin arzikin duniya. A makon da ya gabata tsohon shugaba kasar ta Sudan Omar Hassan Ahmad al-Bashir ya sake karbar wata wasika mara dadi a gidan yari. Wanda ya aike da wasikar shi ne Sa'id al-Yazal Muhammad Sarri, babban mai gabatar da kara na kasar. Lauyan yana zargin al-Bashir da karya dokar kundin tsarin mulkin kasar na 1989.

Tsohon shugaban na kama karya wanda sojoji suka hambarar da mulkinsa bara a ranar 11 ga watan Afrilu, bayan gagarumar zanga zangar gama gari ya fara kallon tasku da ke tunkararsa. Tuni dai ya fara dandana wannan hali inda a watan Disamba aka yanke masa hukuncin daurin shekaru a gidan yari, bisa laifin cin hanci da rashawa.

Sudan Präsident Umar Hasan Ahmad al-Baschir
Hoto: Reuters

Bugu da kari gwamnatin wucin gadi da aka kafa wadda ta kunshi sojoji da fararen hula, a watan Fabrairu sun amince su mika shi ga kotun shari'ar manyan laifuka ta duniya da ke Hague, kan zargin aikata laifukan yaki a Darfur.

Juyin-juya halin na Sudan ya gudana cikin hanzari bayan da hukumomin tsaro suka mara baya ga yan zanga zangar da kuma samun karin tagomashi daga kungiyar Tarayyar Afirka da kuma kungiyar Tarayyar Turai EU.

Babban rashin jin dadi da ba za a manta da shi ba, shi ne kisan gillar da aka yi wa jama'a a ranar uku ga watan Yuli shekarar 2019, inda aka harbe masu zanga-zanga fiye da dari daya a rana guda. Amal wata wadda aka karya mata hannu a yayin zanga-zangar, ta bayyana halin da ta sami kanta ciki a wancan lokaci.
 

"A lokacin da suka karya min hannayena sai suka fara duka na aka, na fadi kasa, bayan da na fadi a kasa sai mutanen suka zo suka rika tattaka ni da kafa suna zagi na. Daya daga cikinsu ya tambaye ni me nake da shi sai na ce masa hannayena a karye suke, sai yace hannayenki ba a karye suke ba, babu wanda ya karya miki hannu."

BG Frauen im Sudan
Hoto: Getty Images/AFP

A ranar 5 ga watan Juli 2019 sojoji da farar hula suka cimma yarjejeniya ta rabon mukamai. Jagoran sojin Muhammed Hamdan wanda ake daukarsa a matsayin mai sassaucin ra'ayi, ya yi wa 'yan kasar jawabi inda ya jaddada cewa.
 
" Yace muna so mu tabbatar wa da dukkan baraden siyasa da kungiyoyin yan bindiga da dukkan matasa maza da mata wadanda suka shiga wannan fafutukar kawo sauyi, cewa wannan yarjejeniya ingantacciya ce ba ta tsame kowa ba kuma ta adalci ga muradin jama'ar Sudan da gwagwarmayarsu ta juyin juya hali". 

A takaice akwai kyakkyawar fata ta sauyi a Sudan kamar yadda wani masanin al'amuran Sudan Jonas Horner kuma kwararre a cibiyar nazarin al'amuran kasa da kasa ya nunar a watan hira da aka yi da shi a watan Disamba.

"Yace hakika ana iya cewa wannan sauyi ne baki daya na daukacin al'amura a Sudan kama daga hukumomi zuwa yanayin rayuwar al'umma."

Kasar Sudan har yanzu tana daga cikin kasashe da ke fama da mastin tattalin arziki, kuma daya daga cikin kasashe goma da ke fama da kantar bashi a duniya, sannan ga tashin gwauron zabi na farashin kayayyaki.

A yanzu dai kamar sauran kasashe a fadin duniya, Sudan ita ma an sami bullar annobar cutar Corona a kasar. Babbar fargaba ita ce idan annobar ta barke sosai a kasar cutar za ta kara tabarbara al'amura a kasar da jefa ta cikin halin tsaka mai wuya.