Cikas ga kokarin samar da zaman lafiya a Mali | Labarai | DW | 18.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cikas ga kokarin samar da zaman lafiya a Mali

Tashe-tashen hankula a cikin gida da Najeriya ke fama da su, ya sa hukumomin kasar janye dakarun kasar da ke Mali.

Hukumomin Najeriya sun fadi - a wannan Alhamis (18.07.13) cewar, kasar za ta janye wasu daga cikin sojojinta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Mali. Ko da shike gwamnatin Najeriya ba ta bayyana dalilin daukar matakin ba, amma shugaban Kungiyar Gamayyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka, kana shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara, ya tabbatar da hakan a lokacin wani taron da shugabannin kungiyar ke ci gaba da yi a Abuja, fadar gwamnatin Najeriya. Shugaba Ouattara, ya ambata cewar, ya samu wasikar neman janye dakarun ne daga shugaba Jonathan na Najeriya, inda ya alakanta hakan da irin abubuwan da ke faruwa a cikin Najeriyar - kanta.

Dama dai Najeriya na da kimanin dakaru dubu daya ne a Mali, wadda ke kokarin farfado wa daga juyin mulkin soji a watan Maris na shekara ta 2012, bayan da wasu masu tada kayar baya suka kwace iko da yankin arewacin kasar. Ita kanta Najeriyar na fama da rigingimu musamman a yankin arewacin kasar, baya ga rikicin siyasar da ke neman kunno-kai a yankin da shugaban kasar ya fito.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe