1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cikas a ƙoƙarin warware rikicin Bangui

December 11, 2013

Shugaba Francois Hollande ya bayyana cewar, tilas ne Faransa ta shiga tsakani a rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya domin kaucewa rincaɓewar lamura a ƙasar.

https://p.dw.com/p/1AXHA
Konflikt zwischen Christen und Muslimen in Zentralafrikanischer Republik 9.12.2013
Hoto: picture-alliance/AP

Shugaban Faransa Francois Hollande, wanda ya isa Bangui, babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da yanmmacin wannan Talatar, tare da rakiyar ministan kula da harkokin wajen Faransa Laurent Fabius, ya kwatanta aikin kwance ɗamarar mayaƙan sa kai a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar da dakarun Faransa ke yi da cewar, yana tattare da hatsarin gaske. Ko da shi ke kuma wajibi ne Faransa ta zama ja gaba wajen sauke nauyin. Ziyarar ta sa dai ta zo ne jim kaɗan, bayan da fadarsa da ke birnin Paris ta ba da sanarwar mutuwar wasu dakarun Faransa biyu da ke yin aikin, inda kuma shugaban ya yi durƙusawar ban girma ga akwatunan da ke ɗauke da gawarwakin sojojin a lokacin ziyarar.

Dama dai masana irinsu Thierry Vircoulon, darektan kula da yankin tsakiyar Afirka a ƙungiyar da ke fafutukar warware rigingimun ƙasa da ƙasa ta International Crisis Group, na da ra'ayin cewar, aikin ba zai kasance da sauƙi ba:Ya ce " A gani na dama ana sa ran samun turjiya, domin kuwa 'yan tawayen ba su taɓa bayyana cewar za su ba da haɗin kai ga shirin kwance ɗamarar ba. A can baya ma gwamnatin wucin gadi ta buƙaci su ajiye makamai kuma su koma barikokinsu, amma hakan bai faru ba."

Hollande besucht Zentralafrikanische Republik 10.12.2013
Ziyarar shugaba Hollande a Jamhuriyar Afirka Ta TsakiyaHoto: picture-alliance/AP

Buƙatar ƙarin dakaru ga Afirka ta Tsakiya

Bayan samun goyon bayan kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya dangane da buƙatar shiga tsakanin ne dai, Faransa ta tura ƙarin dakarun da a yanzu yawansu ya kai dubu ɗaya da 600, inda nan ba da daɗewa ba kuma ake sa ran dakarun Tarayyar Afirka da ke can ya ƙaru daga dubu biyu da 500 zuwa dubu shidda. Amma a cewar Lewis Mudge, jami'in da ke kula da sashen Afirka a Ƙungiyar kare hakkin Jama'a ta Human Rights Watch, wadda cibiyarta ke ƙasar Amirka, dakarun ba su wadatar ba:Ya ce "Dakarun da Faransa da Ƙungiyar Tarayyar Afirka suka tura, kyankyawan mafari ne, amma akwai buƙatar aike wa da dakaru masu yawa domin samun ingantacciyar zaman lafiya, don samun damar kai agaji ga mabuƙata da kuma fara bin tafarkin siyasa wajen warware rikicin."

Zentralafrikanische Republik Michel Djotodia
Shugaba Michel DjotodiaHoto: picture alliance/landov

Sulluɓewar iko daga hannun shugaba Djotodia

A yanzu dai, shugaban wucin gadin ƙasar Michel Djotodia, wanda 'yan tawayen suka taimaka wa ɗare wa bisa madafun iko a cikin watan Maris, ya tabbatar - shi da kansa cewar, akwai waɗanda ba sa yi masa biyayya cikin 'yan tawayen na Seleka. Waɗanda wasu ke cewar, sun ƙunshi mayaƙa daga ƙasashen Chadi da Sudan. Jean-Claude Allard, darektan bincike a cibiyar nazarin dangantakar ƙasa da ƙasa da ke brnin Paris na Faransa, ya ce akwai wata babbar matsalar da ke janyo cikas:Ya ce " Dakarun gwamnati na cikin mumunan yanayin da za a iya kwatanta wa da cewar kamar ma babu su ne sam-sam. Bugu da ƙari kuma, har yanzu akwai wasu sojojin gwamnatin da ke zama su ne ma 'yan tawayen Sekeka." Gabannin Seleka ta shiga fafatawa, wadda ta kai ga kifar da gwamnatin shugaba Bozize dai, 'yan tawayen sun koka game da watsin da hukumomin a birnin Bangui suka yi da yankinsu na arewa maso gabas da ke zama galibin mazaunansa Musulmi ne a ƙasar da mafi rinjayenta mabiya addinin Kirista ne, lamarin da ya sa a yanzu kuma batun addini ya shiga cikin rikicin, wanda ke ci gaba da haddasa mutuwar jama'a, yayin da kiyasi ya nuna cewar, kimanin mutane dubu 500 ne suka tsere daga matsugunansu.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da rahoton da wakilinmu na Nijar Gazali Abdu Tassawa ya aiko mana dangane da halin da 'yan Nijar suke ciki a Afirka ta Tsakiya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu