Cika shekaru 75 da yakin duniya na biyu | Labarai | DW | 24.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cika shekaru 75 da yakin duniya na biyu

A Rasha an gudanar da faretin soji mafi girma a bukukuwan zagayawar cikar shekaru 75 da kawo karshen yakin duniya na biyu.

Sojojin kusan dubu 14 cikin tankoki da jiragen sama na yaki suka gudanar da faretin a birnin Moscow. A cikin jawabin da ya yi shugaba Vladmir Putin ya yi kashedi dangane da yunkurin da kasashen yammacin duniya suke yi na canza tarihin yakin duniyar na biyu a game da irin  rawar da Rasha ta taka a lokacin tarrayar Soviet: '' Al ummar Rasha ta fi kowace tafka asara a loacin yakin da gwamnatin 'yan Nazi wanda ya ce tarryar ta Soviet ta kubtar da kasashen Turai daga mamayar 'yan mulkin Nazi na gwamnatin AdolfHitler.''
 Mutane miliyan 27 suka mutu a Rashar a lokacin yakin duniyar na biyu.