1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cigaban zaɓen jihohi a Jamus

Umaru AliyuFebruary 25, 2008

Zaɓen jihar Hamburgh a Jamus

https://p.dw.com/p/DCzJ
Angela Merkel da Ole Von Beust na jamiiyyar CDUHoto: AP


Jama'iyar da tasha kaye, ko da shike ta sami karin kuri'u a bana, idan aka kwatanta da shekaru hudu da suka wuce, ita ce yar karamar jam'iyar nan ta Free Democrats, wadda duk da karin kashi ɗaya da ɗigo tara cikin ɗari da ta samu, amma bata sami kueri'u misain kashi biyar ciikin dari da take bukata kafin ta shiga majalisar ta birnin Hamburg ba. A daya hannun, jam'iyar Greens ta masu kare muhalli ta sami kashi tara ne da digo shidda cikin dari, ita kuma jam'iyar masu neman canji ta tashi da kashi shidda da digo hudu cikin dari. Magajin garin birnin Hamburg, wanda a lokaci guda shine shugaban gwmanatin jihar tza Hamburg, Ole von Beust dan jam'iyar CDU duk da asarar cikaken rinjayen da yayi a majalisar birnin, amma yace:


Sakamakon zaɓen alamma ce mai karfi ta damar da aka baiwa jam'iya CDU domin taci gaba da mulki. Dangane dfa haka zamu gudanarda shawarwari da jam'iyar SPD da kuma yan Greens. Daga nan zamu ga abin da suke so da sharuddan da zasu shimfida, kafin ku yanke kudiri cikiin gaggawa a game da abokiyar hadin gwiwar mu, a game da matakan da zamu dauka nan gaba.


Jam'iyar Social Democrats, wato SPD da babban dan takarar ta, Michael Naumann, suna ganin sune suika sami nasarar zaɓen a Hamburg ranar Lahadi. Jam'iyar ta SPD ta sami karin goyon baya dfaga masu zabe, kuma tana ma iya kafa gwamnati idan har ta hada kanta dfa jam'iyun Grteens da ta masu neman canji, domin samun rinjayxe a majalisar dokokin ta birnin Hamburg. To amma Naumann yace har yanzu yana nan kan alkawarin da yayi lokacin kampe kafin zaben.


Jam'iyar SPD a Hamburg ba zata hada kanta da jam'iyar masu neman canji ba, ba kuma zata gudanar da shawa5wari da ita ba. Wannan kuwa al'amari ne da ya shafi dukkanin yan jam'iyar SPD a wannan birni. Ina da ra'ayin cewar daya daga cikin al'amuran da jam'iyar Social Democrats tayi suna a kansu a tsawon fie da shekaru dari na rayuwar ta, shine rike alkawari.


Naumann ya kwatanta kansa ne a matsayin mai cikakken adawa da tafarkin kwaminisanci, kuma a lokacin da yake kampe ma ya sha amfani da kalmar Njet, wato a'a da harshen Rashanci.


A daura da haka, babbar yar takarar jam'iyar ta masu neman canji, Dora Heyenn, wanda ta dade cikin jam'iyar SPD tafin ta fice, tace batun hada kai da wasu jam'iyu domin neman kafa gwamnati ma bai taso ba domin kuwa kamar yadda tace:


Tuni muna nunar a fili cewar mun fi son kasancewa yan adawa, kuma lokacin damkuka lura cewarf jam'Iyun SPD da Greens sun dauki abubuwa da dama daga garemu, mun yi tunanin ko ba zai dace mu goyon bayan kafa gwamnatin hadin gwiwa ta wadnanan jam'iyu biyu ba. Bamu dai tsaida kudiri ba tukuna, saboda haka, kowa ya zura ido ne ya ga abin da zai faru a Hamburg, saboda mun hana yiwuar kafa gwamnatin hadin gwiwa ta CDU da FDP, kuma gwamnatin hadin gwiwa ta SPD da GReens ma abu ne da ba zai yiwu ba.


To hakan kuwa abu ne da ya tayar da hankalin yan jam'iyar Greens matuka, domin kuwa jam'iyar tayi fatan hada gwia ne da SPD domin kafa gwamnati a Hamburg. A yanzu kuwa, yan jam'iyar kalilan ne suke farin cikin yiwuwar hadin kai tare da CDU. Christa Goetsch, babbar yar takara ta jam'iyar Greens tare ko kadan ba zata ji ddadin kafa gwamnatin hadin gwiwa da CDU ba, to amma:


Jam'iyu na democradiya an saba suna tattaunawa da junan su, wnanan kuma ab ne da zamu yi tsakanin mu. Sauran duk abin da zai biyo baya, zai dogara ne ga wadannan shawarwari, saboda abubuwan da zamu tattauna kansu a bayan zaben basu wuce wadanda mukai ta magana kansu kafin zaben ba. Al'amura masu wahala daga cikin su sun hada har da makomar tashar makamasdhin nuclear ta Moorburg da manufofin bayar da ilimi a jihar.


Ita kuwa jam'iyar Free Democrats, kamar dai shekaru hudu da suka wuce bata sami shiga majalisar ta GHamburg ba, saboda haka nan da shekaru hudu masu zuwa, al'amuran mulki ko siyasar Hamburg za'a tafiyar dasu ne ba tare da ita ba.