Cigaba da yaƙin neman zaɓe a Amirka | Labarai | DW | 02.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Cigaba da yaƙin neman zaɓe a Amirka

'Yan takarar shugabancin Amirka wato Barack Obama da abokin hammayarsa Mitt Romney na cigaba da zawarcin ƙuri'un al'ummar ƙasar kwanakin huɗu kafin zaɓe.

U.S. Republican presidential nominee Mitt Romney (L) and U.S. President Barack Obama gesture towards each other during the second U.S. presidential debate in Hempstead, New York, October 16, 2012. REUTERS/Mike Segar (UNITED STATES - Tags: POLITICS ELECTIONS USA PRESIDENTIAL ELECTION TPX IMAGES OF THE DAY)

TV-Duell Barack Obama und Mitt Romney Wahlkampf USA

Shugaba Obama ya ziyarci Wisconsin inda al'umma su ka yi ta jinjina masa dangane da matakan da ya ɗauka yayin da mahaukaciyar guguwar Sandy ta afkawa gabar ruwa da ke gabashin ƙasar.

Ɗan takarar Republican kuwa Mitt Romney ya ziyarci Virginia inda ya shaidawa masu kaɗa ƙuri'a cewar gwamnatin da zai kafa in har sun zaɓe shi za ta kawo sauyi yayin da ya ce sake zaɓen Obama a matsayin shugaban ƙasa ba zai haifawa ƙasar komai a illa koma baya na tattalin arziki.

A daidai lokacin da 'yan takarar biyu ke cigaba da yaƙin neman zaɓe, a gefe guda magajin garin New York Micheal Bloomberg ya ce ya yanke shawarar marawa Obama baya duba da yadda Obama ya tashi haiƙan don sanya idanu kan abubuwan da ka je su koma yayin da guguwar Sandy ta bayyana a ƙasar. A baya dai Mr. Bloomberg ɗan jam'iyyar Republican ne kafin daga baya ya zama ɗan indifenda, ya kuma sha sukar shugaba Obama kan manufofi daban-daban na shugaban.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Mouhamaddou Awal