1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cigaba da neman kafa kasar Falasdinu

Lateefa Mustapha Ja'afarJanuary 5, 2015

Shugaban Falasdinu ya ce za su sake mika daftarin bukatarsu na neman Isra'ila ta kawo karshen mamayar da ta ke musu nan da shekaru uku ma su zuwa.

https://p.dw.com/p/1EFB8
UN Vollversammlung 26.09.2014 - Mahmud Abbas
Hoto: Reuters/Mike Segar

A makon da ya gabata dai Falasdinu ta mika daftarin bukatar gaban kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na neman Isra'ilan ta kawo karshen mamayar da ta ke yi musu nan da shekara mai zuwa, sai dai daftarin bai samu nasarar wucewa ba biyo bayan gaza samun kuri'un kasashe taran da ake bukata daga cikin kasashe 15 da ke zaman mambobin kwamitin. Duk da wannan nasara da suka gaza samu, Shugaba Mahmud Abbas Falasdinawa ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba domin kuwa za su ci gaba da yin fafutukar kwatowa kansu 'yanci daga Isra'ila ke ci gaba da mamaye Falasdinun ya na mai cewa "ba za mu fasa ba har sai kwamitin sulhu ya amince da bukatarmu kuma komai dadewa zai amince."

Israel Benjamin Netanjahu Porträt 28. Dez. 2014
Firaministan Isra'ila Benjamin NetanyhuHoto: Reuters/G. Tibbon

Kasashe takwas ne dai suka kada kuri'ar amincewa da daftarin farko da Falasdinawan suka gabatar bisa jagorancin kasar Jordan, yayin da Amirka da Austaraliya suka hau kujerar na ki. Kashe biyar sun kauracewa kada kuri'a ciki kuwa har da Birtaniya da Najeriya, matakin da mahukuntan na Falasdinu suka nuna damuwarsu a kai suna mai cewa Najeriyar ta basu kunya. Duk da kasa samun nasarar tsallakewar da suka yi da kuri'a daya tilo, shugaban Falasdinawan ya ce ba wai kasawa suka yi ba, inda ya kara da cewar "muna sake nazari za kuma muyi nazarin tare da kawayenmu musamman kasar Jordan, saboda suna kusa da mu kuma sun damu da halin da muke ciki matuka."

A nata bangaren, Isra'ila ta ce za ta dauki tsattsauran matakai a kan Falasdinu in har ta cigaba da yin gaban kanta wajen kwatarwa kanta 'yanci. Matakin farko da Isra'ilan ta dauka kuwa shi ne yadda Shugaba Benjamin Natanyahu na Isra'ilan ya sha alwashin sanya takunkumi a kudin harajin Falasdinawan da yawansu ya kai dalar Amirka miliyan 125. A cewar ministan tsare-tsare na Isra'ilan Yuval Steinitz matakin ya zamo wajibi domin kuwa Falasdinun na yin gaban kanata abin da kuma ya sabawa yarjejeniyar da suka cimma a birnin Oslo.

Felsendom Moschee in Jerusalem Altstadt Ostjerusalem Israel Palaestina
Masallacin birnin KudusHoto: DW/Diana Hodali

A hannu guda kuma sakatare janar na kungiyar kasashen Musulmi ta OIC Iyad Amin Madani ya ayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin yawon bude idanu na Musulunci a shekarar da muke ciki ta 2015 inda ya bukaci Musulmin duniya baki daya da su ziyarci birnin tare da yin salloli da addu'oi a masallacin Kudus. A wannan Litinin din ne ake saran Madani zai ziyarci Masallacin na Kudus da ke zaman masallaci na uku mafi tsarki ga Musulmi.