1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cibiyar Rancen Kudi Domin Ayyukan Rayawa

June 29, 2004

Sakamakon ayyukan cibiyar ba da lamuni ta Jamuas domin hada-hadar raya kasashe masu tasowa a shekarar da ta wuce

https://p.dw.com/p/Bvib

Cibiyar ba da rancen kudi domin ayyukan rayawa tana samun kwangila ne daga gwamnati domin ma’amalla da kasashe masu tasowa, sannan ita kuma kungiyar taimakon raya kasa dake karkashinta take ba da rancen kudi ko sayen hannayen jari da rufa wa kamfanonin Jamus dake zuba jari a kasashe masu tasowa. A halin yanzu haka cibiyar rancen kudin ta Jamus tana da hannu a shirye-shirye kimanin 1400 a kasashe 106 masu tasowa. A shekarar da ta wuce an samu karuwar kashi 20% ga yawan kudaden na rance da cibiyar ke bayarwa. Kuma ko da yake ma’aikatar taimakon raya kasashe masu tasowa ta yi kari akan abin da ta saba gabatarwa na taimako, amma ita ma cibiyar ta samu kafar dogara da kanta sakamakon matakan da gwamnati ta dauka na cike gibin da take fama da shi. Kasashe masu matsakaicin ci gaba daga rukunin kasashe masu tasowa sune suka fi cin gajiyar wannan bunkasar da cibiyar ta samu. A daura da haka, babban aikin da cibiyar ta sa gaba shi ne ba da gudummawa iya gwargwado a matakan yaki da talauci a kasashe masu tasowa. Ta kan yi amfani da kudadenta wajen karfafa makomar cibiyoyin dake taka muhimmiyar rawa ga bunkasar tattalin arzikin kasashen da lamarin ya shafa da kuma ba wa talakawan kasa wata dama da shiga a rika damawa da su a manufofi na siyasa da tattalin arziki da zamantakewar jama’a. A lokacin da yake bayani game da haka Wolfgang Kroh wakilin kwamitin zartaswa na cibiyar dake kula da manufofin taimakon raya kasashe masu tasowa karawa yayi da cewar:

Tilas ne a tantance abubuwan da za a ba wa fifiko ta la’akari da yawan matsaloli da wahalhalun dake akwai a bangare guda da kuma karancin kudin da ake fama da shi a daya bangaren, domin ta haka ne kawai za a cimma burin da aka sa gaba na kayyade yawan ‚yan rabbana ka wadata mu da misalin kashi 50% na da shekara ta 2015. Matakan yaki da matsalar talaucin zasu cimma nasara ne kawai idan su kansu wadanda lamarin ya shafa suka samu kafar shiga a dama da su akan manufa.

Ita ma kungiyar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus dake karkashin tutar cibiyar ta rancen ayyukan rayawa ta bayyana farin cikinta game da sakamakon ayyukanta a shekarar da ta wuce, inda ta samu bunkasar kashi 10% ga kasafin kudinta. Tayi gabatar da jumullar kudi Euro miliyan dubu biyu da dari hudu ga kamfanoni 472 dake gudanar da ayyukansu a kasashe masu tasowa. Bisa ga ra'ayin kungiyar, wadannan kamfanoni masu zaman kansu suna ba da kyakkyawar gudummawa a matakan yaki da talauci a kasashe masu tasowa saboda suna samar da guraben aikin yi ga jama'a da giggina makarantu da wuraren kiwon lafiya ga ma’aikatansu.