Ci-gaban tattaunawar taron Global Media Forum | Siyasa | DW | 01.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ci-gaban tattaunawar taron Global Media Forum

Taken taron na bana wanda tashar Deutsche Welle ke shiryawa a kowace shekara zuwa ga 'yan jaridu na duniya shi ne gudunmawar da masu ma'amalla da kafofin yaɗa labarai ke bayarwa.

Babban abin da ake ci gaba da tattaunawa a kai shi ne na hanyoyin da sauran mutane ke bayar da gudunmawa wa kafofin yada labarai, musamman sabbin kafofin da ake samu ta Internet.

Ƙaruwa da mahalarta taron suka samu a taron na kwanaki uku

GMF Global Media Forum 2014

Mahalarta taron GMF da ke gudana a Bonn

Shin ga mahalarta wannan taro wani abu suka koya da zai taimaka wa aikin jaridu da suke yi, musamman ga kafofin yaɗa labarai na Afirka, kuma ƙasashen Afirka da aka bar su a baya za su iya zabura domin shiga cikin sauran dangi.

Halima Umar Sale da Hauwa Abubakar Ajeje na Muryar Najeriya sun ce taron zai taimaka sossai ga bunƙasa aikin da suke yi a Afirka. Sannan Ibrahim Malam Goje na gidan rediyon Bauchi, ya ce cuɗanya da sauran 'yan jaridu na duniya ya faɗaɗa masa ilimi da ƙara gogewa kan aikin jarida.

Minisatn harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier yana cikin waɗanda suka gabatar da ƙasida kuma ya yi nuni da irin sabbin ƙalubalen da duniya ta samu kanta a ciki.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da rahoton da Ramatou Issa Wanke ta haɗa mana a kan taron ita ma, da hirar da Abdourahamane Hassane ya yi da ministan watsa labarai na Nijar Yahouya Sadissou Madobi ɗaya daga cikin mahalarta taron.

Mawallafi : Suleiman Babayo
Edita : Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin