Ci gaban rikici a Irak | Labarai | DW | 23.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban rikici a Irak

A ƙasar Iraƙi a na ci gaba, da yaƙe yaƙe tsakanin yan sunni da yan chi´a, a sakamakon harin da wasu mutane, da ba a tantance ba, su ka kai ga ɗaya ,daga mahimman wuraren ibadar yan chi´a.

A sahiyar yau rahotani daga assibitocin ƙasar sun ce an ƙara kai gawwawakin wasu mutane 80.

A baki ɗaya, mutane kimanin 200, su ka rasa rayuka, daga ɓarkewar rikicin zuwa yanzu.

A birane daban daban, yan chi´a na kai hare haren ramuwar gayya ga massalatan yan sunni, da su ke zargi da ruguza wurin ibadar na su.

Shugabanin ɗarikar sunni, sun tuhumi jagoran yan Chi´a, Ayatollah Ali Sistani,da ƙara rura wutar wannan rikici.

Kazalika, sun ƙauracewa taron da gwamnati ta kira, tsakanin ɓangarorin 2, domin maido da zaman lahia.

Gwamnati, ta kafa dokar hanna hitar dare, daga ƙarfe 8 har zuwa 6 na sahe.

Yau ne, dokar zata fara aiki , bugu da ƙari, an ƙarfafa mattakan tsaro a faɗin ƙasar baki ɗaya.

Wannan sabin tashe tashen hankulla da su ɓarke a ƙasar Iraƙi sun rutsa da ma´aikata 3 na gidan Talbajan Al Arabiya, da su ka rasa rayuka, kazalika sojojin Amurika 4 sun sheka lahira a Hauwija dake arewancin Bagadaza, a yinin yau.

Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen larabawa da Majalisar Ɗinkin Dunia, sun yi Allah wadai da wannan sabin rigingimu da ke abkuwa a Iraƙ.