Ci gaban neman jirgin AirAsia | Labarai | DW | 06.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban neman jirgin AirAsia

Gwanayen linkaya a cikin teku na ci gaba da aikin neman a yau Talata, a wani aiki da ake ganin za su kai ga wani abu da ake tsammani jirgin AirAsia ne da ya fada teku tare da fasinjoji 162.

A cewar shugaban aikin ceton na Indonesiya Bambang Sulistyo, a yau yanayi ya inganta saboda haka suna fatan zasu kai ga wannan jirgi , inda ake tsammanin ganin wasu fasinjojin da suka rasu a cikinsa.

Jami'an aikin ceto sun bayyana a ranar Asabar cewa na'urar da ke taimakawa wajen gano abubuwan da suka bace a zurfin teku, ta nuna alamar cewa ta gano wasu manyan abubuwa guda biyu da ake saran a sami jirgin cikinsu.

Ya zuwa yanzu dai mutane 37 ne aka gano su a mace, bayan hadarin wannan jirgi da ya bace a kan hanyarsa daga Surbaya zuwa Singapore a ranar 28 ga watan Disambar bara.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu