Ci-gaban fadace-fadace a birnin Benghazi | Labarai | DW | 16.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci-gaban fadace-fadace a birnin Benghazi

A kalla mutane 17 ne suka rasu cikin awoyi 24 sakamakon rikicin da ya hada sojojin kasar ta Libiya, da mayaka masu rajin kafa shari'ar Muslunci a wannan kasa.

Babban asibitin birnin Benghazi ya sanar cewa ko a daren jiya Laraba (15.10.2014) an samu gawawaki biyar, abun da ya kai adadin wadanda suka mutu ga mutune 17. Wasu daga cikin 'yan kasar masu dauke da makammai, sun kasance tare da mayakan Janar mai ritaya Khalifa Haftar da suka kai wani sabon samame, a kokarin da suke na kwace wannan birni daga hannun mayakan na Ansar Asharia. A ranar ta Laraba ce dai, mayakan dake biyayya ga Janar Haftar kuma masu samun goyon bayan sojojin kasar, suka bada sanarwar samun nasarar kwace ofishin mayakan masu tsauraran ra'ayin addini dake wajan birnin na Benghazi.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohammed Abubakar