Ci gaban arangama a taron G20 | Labarai | DW | 07.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaban arangama a taron G20

An sake shan artabu tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sanda a taron G20 da ke gudana a brnin Hamburg.

 'Yan sanda da ke kula da tabbatar da tsaro a wajen taron na G20 sun bukaci da a kawo musu dauki, domin tinkarar masu fafutuka da ke yin zanga-zangar adawa da taron tun a farkon wannan mako. Wadanda suka sake yin wani gangamin a yau, inda aka sake shan artabu tsakanin su da jam'ian tsaro.