1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da zubar da jini a Najeriya

April 14, 2014

Hari da aka kai da bama-bamai da sanyin safiyar Litinin a Abuja ya hallaka akalla mutane 71. Sai dai Najeriya ta sha alwashin kawo karshenwadannan hare-haren.

https://p.dw.com/p/1Bhii
Hoto: picture alliance/AP Photo

Shugaba Goodluck Jonathan ne ya bayyana hakan yayin ziyarar gani da ido da ya kai a tashar mota ta Nyanya da ke Abuja babban birnin kasar inda wani hari da aka kai da bama-bamai da sanyin safiyar yau ya hallaka mutane 71. Da yake nuna takaicinsa kan harin Shugaba Jonathan ya ce an yi asarar rayuka da dama kuma batun Boko Haram abun takaici ne a tarihin Najeriyar inda ya sha alwashin cewa za a kawo karshen hare-haren domin kuwa batun na Boko Haram na dan lokaci ne.

Tun da farko a jawabin da ya yi ga manema labarai kakin rundunar 'yan sandan Tarayyar Najeriyar Frank Mba ya tabbatar da cewa mutane 71 sun rasa rayukansu yayin da wasu 124 suka jikkata a harin da aka kai da sanyin safiyar yau a unguwar Nyanya dake Abuja babban birnin kasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal