Ci gaba da zaman Scotland a Birtaniya | Siyasa | DW | 19.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ci gaba da zaman Scotland a Birtaniya

Kasashen Turai sun bayyana farin cikinsu a kan nasarar da masu adawa da ballewar yankin Scotland daga Britaniya suka samu a zaben jin ra'ayin jama'a da aka gudanar.

Sai dai kuma kungiyoyi da ke gwagwarmayar neman mulkin kai a wasu kasashen Turai kamar su Spain da Belgium da Italiya sun bayyana bakin cikinsu a kan rashin nasarar da masu neman 'yancin yankin Scottland din suka yi. Duk da yake wasu na ganin cewa suma wadannan kungiyoyi da ke neman ballewar yankunansu a wasu kasashen Turai, kamata yayi su baiyana farin ciki bisa ganin cewar takwarorinsu na Scotland da kyar aka kayar dasu a zaben na jin ra'ayin Jama'a, ganin cewan duk da yake sun sha kaye sun samu alkawura daga gwamnati a London na cewar nan gaba zasu sami karin iko na tafiyar da al'amuransu da kansu. Bugu da kari kuma, kungiyoyin masu neman balewa a nahiyar Turai an yi musu alkawarin cewar nan gaba suma zasu sami damar kada kuri'ar jin ra'ayi dangane da ko al'ummar yankunansu na bukatar samun mulkin kansu.

EU Gipfel Brüssel 16.7.2014 Schulz

Shugaban majalisar Turai Martin Schulz

Matsin lamba ga gwamnatocin Turai

Hakandai na nufin matsin lamba yana karuwa kenan a kan gwamnatocin kasashen Turai, duk da kayen da masu neman 'yanci suka sha a Scotland. Hukumar kungiyar hadin kan Turai da majalisar Turai sun bayyana jin dadinsu a game da sakamakon zaben na Scotland, inda shugaban majalisar Turai Martin Schulz yace yana farin cikin sakamakon ne saboda dalilai biyu:

Yace: "Da farko dai na yi imanin cewa zaben na jin ra'ayin jama'a ya gudana ne bisa dacewa da manufofin dimokaradiyya na cikin gida na Britaniya, inda gwamnatin Tarayyar gaba daya ta amince ta kuma ba da izinin kada wannan kuri'a. Na biyu kuma shine ganin cewar yadda zaben ya gudana ya gamsar da ni, na kuma ji dadin irin sakamakon da aka samu".

Hukumar kungiyar hadin kan Turai bisa manufa kamata yayi ta zama 'yar ba ruwanmu a batun zaben na jin ra'ayin jama'ar a Scotland, to amma tun kafin a gudanar da shi shugaban hukumar Jose Manuel Barosso ya bayyana tsoron abin da zai biyo baya idan har masu zaben suka amince da ballewar yankin dama samun 'yancin cin gashin kansa.

Matakan kungiyar hadin kan Turai

Merkel und Rajoy 25.08.2014 in Santiago de Compostela

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

Yace: "Idan sabuwar kasar Scotland ta na son shiga kungiyar hadin kan Turai sai ta sake kafa sabon tushe na bin duk hanyoyin da aka saba kafin a karbe ta a kungiyar".

Wannan dai shine matakin da janar sakatare na kungiyar tsaro ta NATO Ander Fogh Rasmussen ya bayyana, inda yace karbar 'yantacciyar kasar Scotland a kungiyar ba zai zama abu mai sauki ba. Ita kuwa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta fito fili ta baiyana jin dadinta dangane da sakamakon da aka samu a zaben na Scotland.

Tace: Tun da farko na ki tsoma kaina ko kuma baiwa masu kada kuri'a a yankin na Scotland wata shawara a kan wannan al'amari na zaben raba gardama. Saboda haka abin da zan fadi kawai shine ina mutunta sakamakon da aka samu tare da murmushi da jin dadi".

A nata bangaren, kasar Spain da 'yan Kataloniya ke gwgwarmayar neman 'yancin yankinsu a arewacin kasar ta nuna jin dadinta ne dangane da yadda 'yan Scotland suka nuna kyamar ballewar yankinsu daga Britaniya. Firaminista Mariano Rajoy yace kasarsa tana matukar farin ciki da wannan sakamako. Bayan da aka sanar da sakamakon kuri'ar ta jin ra'ayi darajar kudin Ingila wato Fam ta karu nan take a kan sauran manyan kudade kamar dalar Amirka da Euro a kasuwannin hada-hadar kudi na duniya.

Sauti da bidiyo akan labarin