Ci gaba da tsare ′yan fafutuka a Turkiya | Labarai | DW | 18.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da tsare 'yan fafutuka a Turkiya

Wata kotun Turkiya ta ba da umurnin a wannan Talata ci gaba da tsare wasu 'yan fafutukar kare hakkin dan Adam su shida da suka hada da daraktan Kungiyar Amnesty International a Turkiya Edil Eser a gidan kurkuku.

Wata kotun Turkiya ta ba da umurnin a wannan Talata ci gaba da tsare wasu 'yan fafutukar kare hakkin dan Adam su shida da suka hada da daraktan Kungiyar Amnesty International na kasar ta Turkiya Edil Eser a gidan kurkuku.

A ranar biyar ga wannan wata na Yuli ne a tsakiyar wani taron bayar da horo kan fasahar amfani da Intanet, mahukuntan kasar ta Turkiya suka kame wasu 'yan fafutukar kare hakkin dan Adam na kasar ta Turkiya su takwas tare da wani dan kasar Sweden da kuma wani Bajamushe da ke bayar da horon, a bisa zarginsu da aikata muggan ayyuka da suna wata Kungiyar ta'adda da amma mahukuntan Turkiyar ba su bayyana sunanta ba. 

Daga bisani an saki hudu daga cikinsu, amma aka ci gaba da rike sauran mutanen shida da suka hada da 'yan asalin kasashen na Turai su biyu wadanda kotun ta bada a wanann Talata umurnin ci gaba da tsare su.