Ci gaba da takurawa ′yan jarida a Masar | Labarai | DW | 28.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da takurawa 'yan jarida a Masar

Gwamnatin kasar Masar na ci gaba da matsawa 'yan jaridu, musamman wadanda ke nuna gazawar gwamnatin wajen biyawa talakawa bukatunsu.

Shugaban kasar Masar Muhammad Mursi ya bayyana rufe wata kafar yada labarai mai zaman kanata a kasar mai suna al-Faraeen, bisa zargin ta da yada labaran karya.

Haka nan ma wata kotu ta tuhumi mamallakin gidan talabijin na CBC Mohammed al-Amin, da laifin kin biyan haraji tare kuma da hana shi fita daga kasar, kwana guda bayan da Shugaba Mursi ya fito karara ya na sukansa.

A bangare guda kuma 'yan adawa a kasar na ci gaba da sukan gwamnatin Mursi, inda suke daukar gwamnatin a matsayin wadda take dakile ci gaba da kuma wargatsa kasar.

'Yan adawar dai sun shirya gudanar da wata gagarumar zanga-zangar kin jinin gwamnati a jibi Lahadi idan Allah ya kaimu, yayin da suma a nasu bangaren masu goyan bayan Shugaba Mursi suka shirya gudanar da zanga-zangar nuna masa kauna.

Maawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu