Ci gaba da ruwan boma-bomai a Gaza | Labarai | DW | 30.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da ruwan boma-bomai a Gaza

Isra'ila na ci gaba da yin ruwan boma-bomai kan fararen hular yankin Zirin Gaza duk kuwa da shelanta tsagaita wuta da ta yi.

Ma'aikatar lafiya ta yankin Zirin Gaza ta tabbatar da mutuwar Palasdinawa 17 sakamakon harin da dakarun Isra'ila suka kai a wani gurin hada-hadar jama'a dake da cunkoso. Wani wakili a ma'aikatar lafiyar ta Gaza Ashraf al-Kidra ne ya sanar da hakan inda ya ce harin ya kuma jikkata wasu da dama. Al-Kidra ya kara da cewa gurin ya kasance a cunkushe biyo bayan samun sanarwar tsagaita wuta daga sojojin Isra'ilan. Kawo yanzu dai babu wani martani da mahukuntan Isra'ilan suka mayar kan wannan batu. Tun da fari dai sojojin Isra'ilan sun sanar da tsagaita wuta na tsahon sa'oi hudu sai dai sun gargadi Palasdinawan da kada su doshi guraraen da dakarun Isra'lan suka mamaye a iya tsahon okacin tsagaita wutar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu