Ci gaba da rikicin siyasa a Pakistan | Siyasa | DW | 16.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ci gaba da rikicin siyasa a Pakistan

Bayan da kotun kololuwa ya bada umurnin kama Pirayim Ministan Pakistan Raja Pervez Ashraf, ana ci gaba da zanga-zanga yan watanni kadan kafin zaben kasar

Ranar Laraba aka shiga rana ta uku ta zanga-zangar dake gudana a kasar Pakistan, inda dimbin jama'a suka taru a biranen kasar dabam dabam suna neman gwmanati tayi murabus, bayan da kotun kololuwa ya bada izinin kama Pirayim Minista Raja Pervez Ashraf, bisa zarginsa da laifukan cin rashawa. A birnin Islamabad, dubban mutane suka amsa kiran da wani babban malami, mai suna Tahir-ul-Qadri yayi domin zanga-zangar da ake ganin ita ce mafi tsanani a kasar ta Pakistan tsakanin shekaru da dama.

Kotun a Pakistan ta bada umurnin kama Pirayim minista Raja Pervez Ashraf da mukarrabansa 16 ne ba tare da wani jinkiri ba saboda zarginsu da aka yi da laifin da ya shafi karbar toshiyar baki a wasu aiyuka na samarwa kasar ta Pakistan injunan karfin lantarki a shekara ta 2010. Hukuncin da ya kotun ta gabatar ya tsunduma kasar cikin halin rashin tabas a fannin siyasa, saboda ko da shike an shirya gudanar da zaben majalisar dokoki a tsakiyar watan Mayu mai zuwa, amma shugaban masu zanga-zangar, Tahir-ul.Qadri yace wajibi ne gwmanatin tayi murabus tun a yanzu a kuma rushe majalisar dokoki, saboda basu da sauran halarci a matsayin wakilan al'ummar Pakistan. Malamin yace gwamnatin ta Ashraf cike take da cin rashawa, ga kuma rashin iya tafiyar da aiyukanta. Lokacin da ya baiyana gaban dubban magoya bayansa ranar Talata, Tahir-ul-Qadri yace ya baiwa gwmanatin wa'adi har zuwa ranar Laraba tayi murabus, a kuma maye gurbinta da gwmanatin wucin gadi da zata yi mulki har zuwa zabe na gaba a watan Mayu.

Tahir-ul-Qadri

Shugaban masu zanga zanga Tahir-ul-Qadri

Masana sun baiyana imanin cewar ba cikin dare daya ne kotun ta ga dacewar bada umurnin kame Pirayim ministan na Pakistan ba. Ana dai zaton kotun yayi amfani da zanga-zangar dake gudana a yanzu ne domin sake tayar da wata tsohuwar ajiya, wato zargin cin rashawa da tuni gwamnatin take fuskanta. Kotun da shugabanta, Ifthikar Mohammed Chaudhry sun dade suna fama da rashin fahimta tsakaninsu da shugaban kasa Asif Ali Zardari. Tun a bara, kotun ta sami nasarar kawar da tsohon Pirayi minista Gilani daga mukaminsa, shima bisa zargin cin rashawa. A daya hannun kuma masu lura da halin da Pakistan din take ciki, sun yi imanin cewar sojojin kasar zasu yi amfani da wannan damar da ta samu, kuma musamman zasu yi amfani da kotun ta kololuwa domin kara karfafa matsayin su a al'amuran siyasar wnanan kasa. Jaridar New York Times ta ambaci masanin siyasa, Najam Sethi yana cewa sojoji zasu yi kokarin ganin a zaben da za'a yi a watan Mayu, shugaban kasa, Zardari da mai goyon bayansa, Nawaz Sharif, shugaban jam'iyar adawa ta Muslim Lig basu cimma burin su na karbe al'amuranm mukin kasar ba. To amma wani dan jarida na Pakistan Saleem Bukhari ya baiyana wani ra'ayi ne dabam a game da matsayin sojojin.

"Yace inda sojojin sun zo da tun a da can ma sun shiga tsakani a rikice-rikicen siyasa da Pakistan tayi fama dasu amma basu yi hakan ba. A gani na, sojojin basu da niya kuma basa ma son tsoma kansu a al'amuran siyasar kasar, misali ta amfani da karfin su. Amma idan al'amuran suka kara muni kuma Pakistan ta fada barazanar mummunan tashin hankali, to kuwa ina ganin alhakin sojojin ne karkashin tsarin muki, su tabbatar da ganin mutunci da yanci da hadin kan Pakistan sun tabbata."

Pakistan Premierminister Raja Pervez Ashraf

Pirayim Ministan Pakistan Raja Pervez Ashraf

Ana dai ci gaba da rade-radi a game da burin da shugaban zanga-zangar ta wannan karo, Tahir-ul-Qadri yake son cimmawa. Malamin dai sananne ne a Pakistan, kuma ya taba shiga harkokin siyasa sosai a wnanan kasa, inda ma ya taba neman mukamin Pirayim minista, sai dai jam'iyarsa mai manufofi na addini, bata sami kujerar da ta wuce kwara daya ba a majalisar dokoki lokacin zaben da aka yi a watan Oktober na shekarata 2002. Wani lauya a Pakistan yace ba abin mamaki bane da Qadri ya sake bullowa yanzu, ya kuma sami goyon bayan jama'a, daidai lokacin da Pakistan take fama da matsalar hauhawar farashin kaya da koma bayan tattalin arziki da rashin gamsuwa a tsakanin yan kasar.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin