Ci gaba da neman baraguzan jirgin Malesiya | Labarai | DW | 23.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da neman baraguzan jirgin Malesiya

Wani Tauraron dan Adam mallakar kasar Faransa, ya gano wani abu mai kama da baraguzan jirgin a yankin tekun Indiya.

A wannan Lahadin ce (23.03.2014) dai hukumomin kasar ta Malesiya suka ce sun samu wasu bayannai daga kasar Faransa, na gano wasu baraguzai da Tauraron dan adam na kasar Faransa ya gano, a nisan Km 2500 a kudu maso yammacin birnin Perth na kasar Australiya.

Yayin wata sanarwa da ya fitar kan wannan labari, ofishin ministan suhurin kasar ta Malesiya ya ce, ana ganin wasu abubuwa masu kama da kayayaki a warwatse, a wata kwarkwada dake bangara kudu a yankin da ake iya samun faduwar jirgi a cikin sa na kasar ta Australiya.

Yau dai fiye da sati biyu kenan da wannan jirgi sanfurin Boeing 777 na kasar ta Malesiya ya yi batan dabo, bayan da ya tashi daga birnin Kuala Lumpur, zuwa kasar China dauke da mutane 239 cikin su kuwa 'yan kasar China mutun 150.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohamed Abubakar