Ci gaba da mutuwar bakin haure a Teku | Labarai | DW | 27.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da mutuwar bakin haure a Teku

Jami'an tsaron da ke gadin gabar teku a Italiya sun sanar da gano gawarwakin bakin haure akalla 50 a wani kwale-kwale da ke safararsu.

Matsalar 'yan gudun hijira da bakin haure a Turai.

Matsalar 'yan gudun hijira da bakin haure a Turai.

Rahotanni sun nunar da cewa jirgin ruwan sintiri na kasar Sweden da ke aiki a hukumar tsaron gabar teku da kasashen Tarayyar Turai suka kafa wato Triton ne ya gano gawarwakin yayin da yake bakin aiki a gabar ruwan Libiya. Sai dai da aka fara ceto wasu bakin hauren 439 a cikin kwale-kwalen kafin daga bisani aka gano gawarwakin a cikinsa. Kungiyar kula da 'yan gudun hijira ta kasa da kasa ta bayyana cewa sama da mutane 2,000 ne suka hallaka a teku cikin wannan shekarar ta 2015 a kokarin da suke na tsallakowa Turai.