Ci gaba da kokarin yakar Boko Haram | Siyasa | DW | 10.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ci gaba da kokarin yakar Boko Haram

Najeriya za ta samar da dalar Amirka milyan 100 ga rundunar hadin gwiwa ta kasashen da ke gabar tafkin Chadi domin yaki da ayyukan ta'adanci musamman na kungiyar Boko Haram.

Sojojin da ke yakar Boko Haram

Sojojin da ke yakar Boko Haram

A yayin taron da ministocin harkokin tsaron yankin tafkin Chadi suka gudanar a Abuja ne suka amince da wannan batu tare kuma da sauran tsare-tsare da ka iya kawo karshen ayyukan kungiyar Boko Haram da ta addabi kasashen yankin da ma tallafawa ayyukan rundunar hadin gwiwa da kasashen suka kafa da kuma wasu shirye-shirye da hukumar kula da tafkin Chadi ta tsara take bukatar a hanzarta aiwatar da su cikin wa'adin watanni 18 masu zuwa.

Samar da kudade domin al'amuran tsaro

Hare-haren ta'addanci a Najeriya

Hare-haren ta'addanci a Najeriya

Rundunar da take da hedikwata a birnin Ndjemena na kasar Chadi tana bukatar dalar Amirka miliyan 30 domin gudanar da ayyukanta a watani 30 masu zuwa, abinda suka bayyana zai taimaka wajen kara kaimi ga sojojin da kasashen suka bada gudummawa domin dakile ayyukan ta'adanci. To ko akwai wani sauyi ne ga dubarun da suke tunanin dauka da a baya matsalar ta'adanci ta nemi zama dan hakin da ka raina a garesu? Alhaji Ismail Aliyu shine babban sakatren ma'aikatar kula da harkokin tsaron Najeriya ga abin da ya ke cewa:

"To wancan lokacin da ake yi Najeriya ke fada amma yanzu an samu hadin kai tsakanin Najeriya da Chadi da Jamhuriyar Nijar da Kamaru da ma Jamhuriyar Benin, duka sun zo da nasu dabarun an hada kai an zama tsintsiya madaurinki daya. To an samu karin dabaru kuma shi za'a ci gaba da shi. Fadan nan fa a Najeriya ake yi dole mu zauna. Najeriya ta yi alkawarin za ta bayar da taimakon dalar Amirka milyan 100, Ingila ita ma ta taimaka. Don haka in Allah ya yarda nan ba da dadewa ba za mu samu zaman lafiya a wadannan kasashen namu."

Ministocin dai sun duba shirin da hukumar kula da tafkin Chadi ta gabatar domin shawo kan matsaloli na talauci da ake dangantasu da rashin tsaro da ya addabi kasashen yankin, shirin da take bukatar a aiwatar da shi cikin gaggawa kuma zai lashe sama da biliyan 38 na kudin Sefa a Najeriya da Kamaru da Chadi. Ko me suka tsara gudanarwa? Injinya Sunusi Imran Abdullahi shine sakataren gudanarwa na hukumar raya tafkin Chadi ya ce:

Boko Haram ta tilastawa mutane kauracewa gidajensu a Najeriya

Boko Haram ta tilastawa mutane kauracewa gidajensu a Najeriya

Shawara ga shugabannin yankin

"Za'a ba wa shugabanin kasashen shawara cewa wadannan ayyukan in an yi su a matsayin aikin gaggawa a wuraren da suka fi fama da wannan matsala na tashin hankali na Boko Haram wanda zai sa mutane su samu daman yin ayyuka. Zamu bada shawarar a fahimtarmu ga yadda ya kamata a yi."

Samun kawance da hadin kai a tsakanin kasashen na zama wata muhimmiyar dama da aka samu musamman tun bayan ziyarar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai kasashen Chadi da Jamhuriyar Nijar. Sai dai duk da samun karin kawance a tsakanin kasashen da ke yankin tafkin Chadin, akwai damuwar sake salon da masu kai hare-hare ke yi a kasashen da ma yiwuwar samun damar sake haduwa daga wuraren da suka bari a baya da kuma kokarin kunno kai na kungiyar IS a yankin Afirka ta yamma.

Sauti da bidiyo akan labarin