Ci gaba da bata kashi a Ukraine | Labarai | DW | 16.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da bata kashi a Ukraine

Rahotanni daga Ukraine na nuni da cewa akalla sojojin kasar shida ne suka rasu sakamakon wani hari da 'yan awaren gabashin kasar masu goyon bayan Rasha suka kai musu.

Kakakin rundunar sojojin Kiev Andriy Lysenko ya sanar da cewa harin an kai shi ne a filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Donetsk da ke karkashin ikon 'yan awaren inda aka hallaka sojojin shida tare kuma da raunata wasu 18. Akalla dai kawo yanzu mutane 11 ne suka rasa rayukansu a yankin gabashin kasar sakamakon sabon bata kashin da bangarorin biyu ke yi a tsakaninsu. Kasashen yamma dai na nuna dan yatsa a kan kasar Rasha bisa zarginta da suke da ci gaba da iza wutar rikicin da yake neman shallake tunanin al'ummomin kasa da kasa.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammed Nasiru Awal