1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da barin wuta a Siriya

November 6, 2014

Sojojin taron dangi da Amirka ke wa jagoranci a yaki da kungiyar 'yan ta'addan IS sun yi barin wuta a kann kungiyar Al-Nusra Front.

https://p.dw.com/p/1DiPM
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Nickel

Kungiyar kare hakkin dan Adam da ke sanya idanu a yakin na Siriya ce ta tabbara da hakan inda ta ce an kashe mayakan na Al-Nusra Front da ke da alaka da al-Qa'ida masu yawa a harin da jiragen yakin suka kai musu a shalkwatarsu da ke arewa maso gabshin Siriyan. Wanna dai shine karo na biyu da sojojin taron dangin karkashin jagorancin Amirka suka kai farmaki a kan wata kungiya da ba ta IS ba da ke yaki a Siriya. Kungiyar ta Al-Nusra Front dai na daya daga kungiyoyin 'yan tawaye da ke yakar gwamnatin Bashar Al-Assad na Siriyan sama da tsahon shekaru ukun da suka gabata.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman