Ci gaba da asarar rayuka a Yemen | Labarai | DW | 02.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ci gaba da asarar rayuka a Yemen

Al'ummar kasar Yemen na ci gaba da fadawa halin tasku sakamakon rikicin kasar da ke kara kazanta.

Yaki ya dai-daita kasar Yemen

Yaki ya dai-daita kasar Yemen

Kwana guda bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana bukatar gaggauta shawo kan halin taskun da fararen hular kasar Yemen ke ciki, ana ci gaba da gwabza kazamin fada a kudancin tashar jiragen ruwa ta birnin Aden.

Wannan na zuwa ne kuma kwana guda bayan da rahotanni suka nunar da cewa wani makamin roka da 'yan tawaye suka harba ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 31 tare kuma da jikkata wasu sama da 100, inda wani hari da 'yan tawayen suka kai a wannan Alhamis din a yammacin garin na Aden ya lalata gidaje masu yawa yayin da 'yan tawaye bakwai da kuma mayakan da ke goyon bayan gwamnatin kasar biyar suka rasa rayukansu.