1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cholera ta hallaka mutane da dama a Juba

May 19, 2014

Mutane tara sun mutu sannan ana yi wa fiye da 100 jinya sakamakon barkewar cutar cholera a Sudan ta Kudu mai fama da rikici tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnati.

https://p.dw.com/p/1C2jL
Flüchtlingslager Tomping in Juba Südsudan
Hoto: DW/Scholz/Kriesch

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce akalla mutane tara sun mutu sannan kimanin 138 na karbar magani a asibiti sakamakon barkewar annobar cutar amai da gudawa ko kuma Cholera a kasar Sudan ta Kudu. Hukumar ta WHO ta ce annobar na nuna alamun yin muni kuma yawan wadanda ke kamuwa da cutar ta Cholera ka iya karuwa. Yanzu haka dai hukumar da kuma sauran kungiyoyin agaji sun dukufa wajen tura magunguna yankin da abin ya shafa da ke kewayen Juba babban birnin kasar. Da ma dai kungiyoyin agaji sun yi gargadi game da wani bala'i ga dan Adam musamman na barazanar matsananciyar yunwa idan 'yan tawaye da dakarun gwamnati suka ci gaba da fada.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu