Chinua Achebe ya mutu | Labarai | DW | 22.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Chinua Achebe ya mutu

A Amurka ne shahararren marubucin adabi na Afirka chinua Achebe ya rigamu gidan gaskiya. Littafinsa mai taken Things fall Apart ne ya fi samun karbuwa a Afrika da duniya.

Nigerian author Chinua Achebe on Oct. 13, 2002, in Frankfurt, Germany. Achebe won the 2007 Man Booker International Prize for fiction in London, Wednesday June 12, 2007, beating nominees such as Philip Roth, Margaret Atwood and Ian McEwan.(AP Photo/Axel Seidemann)

Shahararen marubucin adabin nan na nahiyar Afirka wato chinua Achebe ya mutu a daren alhamis zuwa juma'a a birnin Boston na kasar Amurka. Ba a dai bayyana cutar da ta yi sanadinsa ba, amma dai na kusa da danginsa sun baiyana cewa Achebe ya shafe tsawon lokaci ya na fama da rashin lafiya. Chinua Achebe wanda ya shafe shekaru 82 a duniya, shi ne marubucin da ya wallafi littafin adabin Afirka da ya fi samun karbuwa a duniya. Wannan littafin mai suna Things Fall Apart an fassara shi cikin harsuna 50 tare da sayar da miliyon 12 daga cikin wadanda aka buga.

An haifi Chinua Achebe a garin Ogidi da ke cikin jihar Anambra ta Tarayyar Najeriya a shekarar 1930. Tun ya na dalibi ya fara rubuce rubuce a rayuwarsa. Amma kuma littafin da ya fi hadassa kace na ce shi ne wanda ya shafi rayuwarsa da kuma ra'ayinsa kan yakin Biafra da ya rubuta a baya-bayannan.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas