1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Xi Jinping ya yabawa jam'iyyarsa

Abdul-raheem Hassan
October 16, 2022

Shugaba Xi Jinping ya bude taron jam'iyyar kwaminisanci karo na 20, inda ya yabawa jam'iyyar wajen tabbatar da zaman lafiya da kiyaye tsaron kasa wajen shawo kan rikicin Hong Kong a shekara ta 2019.

https://p.dw.com/p/4IFSR
Shugaban China Xi Jinping
Hoto: Jason Lee/REUTERS

Da yake jawabi kan makomar shugabancinsa, Xi Jinping ya nuna alamar sake neman wa'adi na uku tare da cewa ba gudu ba ja da baya a yunkurin hana Taiwan zama kasa mai cin gashin kanta.

"A matsayin martani ga ayyukan 'yan aware na neman 'yancin kai na Taiwan da kuma tsokanar tsoma baki a harkokin Taiwan, mun yi tsayin daka wajen yaki da 'yan aware da kuma katsalandan din da ke nuna azama da karfinmu. don ceto tsarin dunkulalliyar kasar Sin da cikakken yankinta da kuma adawa da 'yancin Taiwan."

Sai dai a nata bangaren kasar Taiwan, ta ce ita ma ba za ta kakkauta ba wajen kare manufarta na zama kasa mai cikakken ikon gwamnati.